Mai Martaba Sarki Sanusi II Ya Kara Gargadi Ga Shugabannin Arewa Akan IlimiSarki Sanusi II yayi wannan bayanine a bikin bude wani dakin bincike a Makarantar nazarin kiwon lafiya na Aminu Dabo da ke Garin Kano a Ranar Litinin. 
Sarkin yace mata na bukatar ilmi kamar yadda maza ke bukata.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya saba kira dai domin inganta  ilmin ‘ya’ ya mata a Yankin Arewa. 

Sannan Sarkin ya yabawa masu makarantar da irin kokarin da suka yi. 
Mai martaba ya kuma kira mutanen Kano da su kara hada kai domin cigaban kasar.
A Kwanakin baya Sarkin Kano Mai girma Muhammadu Sanusi II ya jinjinawa Gwamna Ayo Fayose na Jihar Ekiti domin irin kokarin da yayi na tada harkar ilmin boko a Jihar sa a wani taro a Jami’ar Jihar inda aka ba Sarkin Digirin dakta na ban girma.

You may also like