Mai mota ya kashe mutum ɗaya da raunata bakwai a rikicin Isra’ila da FalasɗinuMota a kife

Asalin hoton, Reuters

An kashe dan yawon bude idanu daya aka raunata wasu bakwai a wani hari da aka kade su da mota a kusa da wurin shakatawa na bakin teku a birnin Tel Aviv na Isra’ila, kamar yadda jami’an lafiya na kasar suka ce.

Dan sanda ya harbe wanda ake zargi da kai harin.

A hoton bidiyon abin da ya faru, a birnin na Tel Aviv ana iya ganin wata mota a kife a wani wuri da ke kusa da wajen shakatawa na bakin teku, yayin da wani dan sandan Isra’ila ya bude mata wuta.

Yan sandan Israi’la sun ce mai motar ya kai hari ne ta hanyar banke mutanen da abin ya rutsa da su.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like