Mai shari’a Wali ya shawarci Buhari ya sasanta Kwankwaso da Ganduje


Tsohon alkalin kotun koli, mai shari’a Abubakar Bashir Wali, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammad Buhari kan ya shiga tsakanin a rikicin siyasar da yaki ci yaki cinyewa tsakanin tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma mutumin da ya gaje shi kuma tsohon mataimakinsa Abdullahi Umar Ganduje.

Da yake magana da jaridar, Daily Trust a wata tattaunawa ta musamman, mai shari’a Wali ya ce ya kamata shugaban yayi gaggawar sasanta Kwankwaso da Ganduje domin a samu kwanciyar hankali a siyasar Kano dama ta arewacin Najeriya baki daya.

Ya bada shawarar cewa bai dace abar rikicin ya cigaba ba domin ba zai haifar wa da yan siyasar da mai ido ba, dama jihar baki daya.

Ya bada shawarar ,” yanayi irin wannan bai dace a barshi ya  cigaba ba. A ganina idan shugaban kasa zai kira yan siyasar biyu yayi musu magana za su iya sasanta tsakaninsu domin kyale mutanen jihar su cigaba da zama lafiya.

“Ina kira ga shugaban kasa da ya sasanta tsakanin Kwankwaso da Ganduje domin samun zaman lafiya mai dorewa a Kano da ma Najeriya baki daya.”

Wali ya koka kan duk  da cewa shi ba dan siyasa bane amma rikicin abun damuwa ne domin yana shafar kimar jihar, arewa da ma kasar baki daya.

Ya shawarci Ganduje da Kwankwaso da su maida takobinsu inda yace siyasa ba batun a mutu ko ayi rai bace. 

You may also like