Maitama Sule Ya Bayarda Shawarar Yadda Za’a Hukunta Barayin Gwamnati


images-8

 

 

Tsohon Minista kuma wakilin Nijeriya a majalisar dinkin Duniya Alhaji Yusuf Maitama Sule ya bayarda shawara game da yadda ya kamata a hukunta barayin gwamnati wadanda hukumar EFCC ke tuhuma da laifukan da suka shafi cin hanci, rashawa da yin sama da fadi da dukiyoyin kasar.

Maitama Sule ya bayyana cewa mafi kyawun hukunci ga wadannan mutane shine a haramta masu shiga harkokin siyasa, da kuma rike mukamin gwamnati kowanne iri.

A wata hira da ya yi a jiya Lahadi, dattijon ya shawarci cewa a kafa doka a majalisa da za ta jaddada wannan haramci saboda ta haka ne kawai za’a iya aiwatar da abun. Ya yi fatan cewa za’a zartar da irin wannan doka nan ba da dadewa ba.

Alhajin ya kuma yabawa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC game da rawar da ta ke takawa wajen daidaita sawukan ma’akatan gwamnati a Nijeriya.

You may also like