Majalisa Ta Amincewa Buhari Ya Amso Bashij Tiriliyan 2.3A karshe dai, majalisar tarayya ta amincewa Shugaba Muhammad Buhari da bukatar da ya sake gabatar mata na neman karbo basussuka har na Naira Tiriliyan 2.3 don gudanar da manyan ayyukan raya kasa.
A zaman da ta yi a jiya Laraba, majalisar ta amincewa Buhari ya karbi basussukan Naira Tiriliyan 1.2 a cikin gida Nijeriya sai Naira Tiriliyan daya daga cibiyoyin lamuni na kasashen waje. Tun a ranar 4 ga watan Oktoba na shekarar da ta gabata ne, Shugaba Buhari ya mika wannan bukata amma majalisar ta ki amincewa.

You may also like