Majalisar Dattawa ta yi Allah wadai da Shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu kan yadda jami’an hukumarsa suka wulakanta Shugaban Kamfanin kera Motoci na Innoson, Mista Innocent Chukwuma ta hanyar cafke shi ba bisa ka’ida ba.
Majalisar ta nemi kwamitin yaki da rashawa kan ya binciki al’amarin. Tun da farko dai, EFCC ta nuna cewa ta dauki matakin cafke Shugaban kamfanin na Innoson ne bayan ya ki amsa gayyatar hukumar kan zargin da ake yi masa na almundahanar Naira Bilyan 1.4 na kudaden inshora.