Majalisar Wakilai ta yi fatali da jadawalin zaben 2019 wanda Hukumar Zabe Mai zaman kanta ta fitar inda majalisar ta fitar da wani sabon tsari kan yadda za a gudanar da zabukan.
A bisa sabon tsarin na majalisar, za a fara gudanar da zaben ‘yan majalisar tarayya, sai zaben gwamnoni da na ‘yan majalisunsu sannan zaben Shugaban kasa wanda za a gudanar a karshe.
A kwanan nan ne dai, hukumar zabe ta fitar da jadawalin zaben 2019 inda ta nuna za a fara zaben Shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya sannan kuma zaben gwamnoni da nasu ‘yan majalisar ya biyo baya.