Majalisa Ta Nemi Buhari Da Ya Gaggauta Tsige Sufeto Janar Na Ƴan Sanda


A zamanta na yau Laraba ne, Majalisar wakilai ta nemi Shugaba Muhammad Buhari kan ya gaggauta tsige Sufeto Janar na ‘Yan sanda, Ibrahim Idiris bisa zargin gazawa wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya.

Haka ma, ‘yan majalisar wakilai daga jihar Binuwai sun nemi kakakin rundunar ‘Yan sanda, Jimoh Moshood bisa kalaman kaskanci da ya yi a kan Gwamnan Binuwai, Samuel Ortom inda ya bayyana Gwamnan a matsayin wanda ruwa-ya-kare masa sannan ya nemi shi kan ya yi murabus bisa kasa tabbatar da tsaron lafiyar al’ummar Binuwai.

You may also like