Majalisa Ta Nemi Buhari Da Ya Mutunta Hukuncin Kotu Kan Tsige Magu


Majalisar Dattawa ta kalubalanci Shugaba Muhammad Buhari kan ya mutunta hukuncin kotu wadda ta tabbatar da cewa majalisar Dattawa na da ikon kin amincewa da Ibarhim Magu a matsayin cikakken Shugaban hukumar EFCC.

Kakakin Majalisar, Sanata Sabi Abdullahi ya jaddada cewa majalisar ba za ta dage takunkumin kin tantance duk wani nadi da Buhari ya yi wanda ke bukatar amincewar majalisar sai ya cire Shugaban EFCC.

A jiya ne dai wata kotun tarayya ta bayyana cewa majalisar Dattawa na da cikakken ikon kin amincewa da Ibrahim Magu a matsayin cikakken Shugaban hukumar EFCC.

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osibanjo ne dai ya ce ba dole ba ne sai majalisar ta tantance Magu kafin ya zama cikakken Shugaban EFCC bayan da majalisar ta ki amincewa da shi bayan da aka tura mata sunansa har sau biyu.

You may also like