Majalisa Ta Nuna Rashin Amincewar Ta Da Tura Sojoji Zuwa Kasar GambiyaMajalisar Dattawa ta nuna rashin amincewa da matakin gwamnatin tarayya na tura sojojin Nijeriya zuwa kasar Gambiya da nufin fatattakar tsohon Shugaban Kasar, Yahya Jammeh wanda ya ki sauka daga kujerar mulki bayan an rantsar da sabon Shugaba, Adama Barrow a jiya Alhamis.
Tun da farko dai, mataimaki Shugaban Majalisar, Ike Ekweremadu ya nuna cewa Shugaba Buhari bai nemi Izinin majalisar ba kafin ya tura sojoji zuwa Gambiya sai dai kuma Shugaban. Majalisar, Bukola Saraki ya ja hankalin majalisar kan cewa doka ya ba Shugaban wa’adin kwanaki bakwai na ya sanar da majalisar bayan tura sojojin.
Kungiyar ECOWAS, ta ce, ta dakatar da sojojin Senegal daga shiga kasar Gambia domin ba da damar sake tattaunawa da Yahya Jammeh, mutumin da yaki sauka daga mulkin kasar bayan wa’adinsa ya kare.
Mai magana da yawun Kungiyar ta Ecowas, Mercel de Souza, ya ce, an ba wa Yahya Jammeh har zuwa karfe 12 na ranar Juma’a da ya sauka daga kujerar shugabancin kasar.
Sai dai kuma har kawo yanzu Mista Jammeh bai ce uffan ba.

Da yammacin ranar Alhamis ne dai dakarun kasar Senegal suka shiga Gambiyar domin tabbatar da cewa Adama Barrow ya karbi mulki a matsayin sabon shugaban kasar.

You may also like