Majalisa Ta Sake Gayyato Sufeto Janar Kan Kisan Binuwai


Majalisar Dattawa ta sake gayyato Sufeto Janar na ‘Yan sanda, Ibrahim Idiris kan yadda ya kasa cika wa’adin da majalisar ta bashi na cafko wadanda suka kashe wasu ‘yan Kabilar Tibi su 73 a jihar Binuwai.

Majalisar ta nuna rashin Jin dadi kan yadda harkokin tsaro ke Ci gaba da tabarbarewa a jihohi Zamfara, Neja da Kano inda matsalar satar mutane da kashe kashe ke ta’azzara.

A dayan bangaren kuma Shugaba Muhammad Buhari ya rubutawa majalisar tarayya inda ya jaddada cewa ya dauki matakan da suka dace kan shawo rikicin Fulani da makiyaya a jihar Binuwai.

You may also like