Majalisa Za Ta Yi Mahawara Kan Ba Jammeh Mafaka A Najeriya 



Majalisar wakilai za ta yi mahawara a kan wani batu na yiwuwar ba Shugaban Gambiya mai barin gado, Yahaya Jammeh mafaka a Nijeriya a matsayin wani mataki na kawo karshen rikicin siyasar da ya dabaibaye kasar.

Da yake gabatar da kudirin, Dan Majalisar wakilai mai wakiltar Jigawa, Sani Zorro ya nuna cewa akwai bukatar na Nijeriya ta duba wannan batu don ganin Yahya Jammeh ya mika mulki cikin ruwan sanyi ga zababben Shugaban kasar, Adama Barrow.

You may also like