Majalisar Ɗinkin Duniya ta nemi jin matsayin kotun duniya kan mamayen Isra’ila a FalasɗinuRyad

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jakadan Falasɗinawa a Majalisar Ɗinkin Duniya, Riyad Mansour yake jawabi ga ‘yan jarida a wannan hoto da aka ɗauka cikin watan Nuwamba

Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ya nemi jin matsayin shari’a daga babbar kotun duniya kan mamayen da Isra’ila ta yi wa yankunan Falasɗinawa.

Ƙudurin wanda ya samu goyon bayan ƙasa 87, sai 26 suka nuna adawa da shi ciki har da Amurka da Burtaniya.

Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya tana da ƙarfin yanke hukunce-hukuncen da wajibi ne a yi musu biyayya, amma ba ta iya tilasta aiki da su.

Ƙuri’ar ta ranar Juma’a, ta zo ne kwana ɗaya bayan rantsar da Benjamin Netanyahu a matsayin firaminista na gwamnatin Isra’ila mafi tsaurin ra’ayi a tarihi.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like