Majalisar Dokokin Jihar Adamawa, ta yi watsi da batun kada kuri’ar nuna goyon baya ga Gwamnan jihar, Umaru Bindow Jibrilla, inda ta ba da hujjar cewa lokacin kada kuri’ar bai yi ba.
Matsayar da ‘yan majalisar suka cimmawa, ta kai ga nasara ne a zauren majalisar a lokacin da dan majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Mubi ta Kudu, Abdurrahman Isa Abubakar, ya tado da batun inda nan take ‘yan majalisar su ka ce a’a.
Da ma ‘yan majalisar su na gudanar da zama kan ‘batun gaggawa’ inda su ka nuna muhimmancin sanya sunaye ga hanyoyi a jihar, musamman ga daidaikun mutanen da su ka ba da gudumuwa wajen samar da ci gaba a jihar.
Ana cikin haka ne kuma mamba mai wakiltar Mubi ta Kudu, Abdurrahman Isa ya shigo da bukatar kada kuri’an nuna goyon baya da karfafa Gwamna Bindo, batun da ‘yan majalisar su ka ce a’a, tare da bayyana aniyar dan majalisar a matsayin neman samun shiga gun Gwamnan.
Wannan batu dai na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ke has ashen cewa jam’iyyar APC mai mulki a jihar na neman darewa gida biyu a tsakanin masu goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da bangaren sakataren gwamnatin jihar, Babachir Dabid Lawal.
Akwai kuma batun ganawar sirrin da aka ce tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi da jiga-jigan APC a jihar.
Cikin wadanda su ka halaraci taron sun hada da Gwamna Umaru Bindow, da mataimakinsa, Martins Babale da Cif Raymond Dokpesi da sauransu, don abin da aka kira da ‘yiwuwar canja sheka zuwa wata sabuwar jam’iyya’.