
Asalin hoton, Getty Images
Wani kwamitin da ke binciken kutsen da aka yi wa ginin majalisar Amurka, Capitol a bara ya yanke shawara cewa a tuhumi tsohon Shugaba Donald Trump da aikata manyan laifuka, ciki har da na yunkurin hambare gwamnati.
Kwamitin da ‘yan jam’iyyar Democrat a majalisar ke jagoranta ya amince da gagarumin rinjaye domin ma’aikatar Shari’a ta kasar ta gurfanar da Mista Trump domin a yi masa shari’a.
Ranar 6 ga watan Janairun 2021 ne dai magoya bayan Mista Trump suka afka wa ginin majalisar, yayin da ake shirin tabbatar da JOe Biden a matsayin shugaban Amurka.
Mista Trump, wanda ya musanta aikata ba daidai ba, ya fitar da wata sanarwa da ke cewa kwamitin na jeka-na-yi-ka ne.
Wannan kwamitin ya shafe wata 18 yana binciken tarzoma da kutsen da suka auku, inda yayin zamansa na karshe a ranar Laraba, ya gabatar da tuhume-tuhume hudu da Mista Trump zai fuskanta:
– Tunzurawa da taimakawa ko bayar da mafaka ga masu son hambare gwamnati
– Hana hukuma binciken gaskiyar al’amarin da suka faru dangane da kutsen
– Kitsa wani shiri na damfarar kasar Amurka
– Kitsa wani shiri domin bayar da wasu bayanai na karya
Sai dai kwamitin ba shi da iko kan ma’aikatar Shari’a, saboda haka ba lallai ba ne a dauki wani mataki kan tsohon shugaban – amma tun bayan boren na watan Janairun bara – ma’aikatar ta fara tunanin gurfanar da shi a gaban kotu.
Kwamitin binciken mai mambobi tara – bakwai daga jam’iyyar Democrat, biyu daga ta Republican – ya fitar da sakamakon binciken nasa ne mai shafi 161 a ranar Litinin.
Ya kuma tuhumi Mista Trump da kitsa boren ta bangarori mabambanta domin yin hana masu zabe cimma burinsa gabanin kutsen da kuma yayin da ake yin sa.
Ranar Laraba kwamitin zai fitar da cikakken rahoton nasa.