Majalisar dattawa ta dakatar da zama na sati biyu saboda kasafin kudin 2019


Majalisar dattawa ta dakatar da zaman da take har na tsawon mako biyu domin bawa ma’aikatu da sauran hukumomin gwamnati damar kare kasafin kudin su na shekarar 2018.

Shugaban majalisar Bukola Saraki ne ya sanar da haka bayan da yan majalisar suka kammala muhawara kan dukkanin abubuwan da suka shafi kasafin kudin  bana.

Saraki ya ce shugabannin ma’aikatu da sauran hukumomin gwamnati dole su byayana domin kare kasafin kudin nasu saboda kwamitin kasafin kuɗi na majalisar ya samu damar kammala aikinsa akan lokaci.

“Mun san cewa jadawalin ya takure sosai shi yasa  zamu dakatar da zaman majalisa  domin fara zaman kare kasafin kudin.”

” Shugaban kwamitin kasafin kudin da sauran yan kwamiti dole su yi sun bi jadawalin.Ina so na nayi amfani da wannan dama na yi gargadi ga hukumomin gwamnati da su tabbatar sun rike rana da kuma lokacin da aka basu,” Saraki yace.

You may also like