Majalisar dattawa a ranar Laraba ta yi kira ga ministan tsaron Najeriya, Mansur Dan-Ali da ya janye kalaman da ya yi na kira ga wasu jihohi da su janye dokar da ta hana kiwo dabbobi a fili.
Yan majalisar sun ce samar da dokar ba shine dalilin da yasa ake kashe-kashen mutane ba a sassa daban-daban na kasarnan.
A ranar Talata, Dan-Ali a wata sanarwa da ya fitar ya yi kira da a dakatar da aiwatar da dokar da ta haramta kiwon dabbobi a fili. Ya ce dakatar da aiwatar da dokar zai rage rikicin da ake fama dashi a wasu jihohi.
Kiran nasa na zuwa ne bayan wata ganawa da shugaban kasa,Muhammad Buhari, ya yi da shugabannin hukumomin tsaron kasar.
Barnabas Gemade, sanata dake wakiltar mazabar Benue maso gabas a majalisar dattawan ya bayyana rashin jin dadinsa ga kalaman ministan inda ya nemi ya janye su.
Ya karfafa cewa manoma da makiyaya suna bukatar kasa amma dole a samar da wata hanya ta yarda za samar da doka domin tabbatar da cewa ana amfani da kasar yadda ya dace.