Majalisar dattawa ta mayar da martani kan fallasar da daya daga cikin yayanta wato,Sanata Shehu Sani ya yi kan kudin da kowane Sanata yake karba a wata.
Bayan an shafe shekaru jama’ar kasa na bukatar sanin kudin da kowane sanata yake karba a kowanne wata a karshe Sani ya bayyana rabe-raben kudin a wata tattaunawa da ya yi a kwanannan inda ya ce kowane Sanata ya na karbar miliyan ₦13.5 a matsayin kudin gudanar da ofishinsa da kuma wasu kudi ₦700,000 na daban.
Amma wannan ba wani sabon abu bane a cewar mai magana da yawun majalisar, Sanata Sabi Abdullahi a wata sanarwa da yafitar.
Abdullahi ya ce “Sani bai bayyana wani sabon abu ba saboda adadin kudin na kunshe ne a kudaden kayayyaki dake cikin kunshin kasafin kudin majalisar kasa “wanda tuni aka bayyanawa jama’a.”
Ya yi watsi da rahotannin da ke cewa sanatocin suna cike da jin haushin Sani saboda wannan tonon silili da ya yi musu.
Idan da mutane sun duba kasafin kudin a tsanake za su ga jerin sunayen abubuwa kamar “Tafiye-tafiye, kula da lafiya da sauransu dukkansu an saka su cikin kunshin kasafin kudin kuma sune kudaden da ake rabawa domin amfanin kowanne Sanata.”
Duk da sanarwar ta Abdullahi, amma Sani ne Sanata na farko da ya taba fadawa jama’a irin kudin da suke karba a kowanne wata.