Majalisar dattawa ta tabbatar da sunayen kwamishinonin zaɓe 7


Majalisar dattawa ta tabbatar da sunayen mutane 7 a matsayin kwamishinoni zaɓen jihohi a hukumar zaɓe ta ƙasa INEC.

An tabbatar da sunayen a ranar Laraba bayan da majalisar dattawa ta amince da rahoton kwamitinta kan hukumar ta INEC.

Da yake miƙa rahoton kwamitin,sanata  Sulaiman Nazif, shugaban kwamitin ya ce cikin sunayen mutane 9 da aka bawa kwamitin ya tantance, takwas ne kawai suka bayyana a gaban kwamitin.

Nazif yace Eric Olowale mutumin da aka zaba daga jihar Osun bai sanar da kwamitin dalilin kin bayyanarsa ba  gaban kwamitin.

Ya ce, Monday Udom Tam wanda aka miƙa sunansa daga jihar Akwa Ibom an dakatar da amincewa da sunansa har sai zuwa zaman majalisar na nan gaba.

Dukkannin mutanen da aka tabbatar sai da suka samu tantancewa daga hukumar tsaro ta farin kaya DSS da kuma hukumar ɗa’ar ma’aikata.

Mutanen da aka tantance sun haɗa da 

  1. Baba Abba Yusuf, jihar  Borno
  2. Lukman Abdulrahman Ajidaba, jihar Kwara 
  3. Segun Agbaje, jihar Ekiti
  4. Cyril Omorogbe, jihar  Edo
  5. Yahaya Bello, jihar Nasarawa 
  6. Emmanuel Alex, jihar Rivers 
  7. Mohammed Magaji Ibrahim, jihar Gombe 

You may also like