Majalisar Dattawan Amurka ta soke dokar afka wa ƙasa da yaƙi



Chuck Schumer

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Shugaban masu rinjaye Chuck Schumer, ya ce lokacin dokar ya wuce

Majalisar dattawan Amurka ta kada kuri’ar sauya dokar da ta bai wa kasar damar kai wa Iraqi hari a shekarar 1992 da kuma 2003, yakin da a yanzu yawanci aka ce kuskure ne.

Wadanda suka goyi bayan matakin, daga jam’iyyar Democrat da kuma wasu ‘yan Republican sun ce yin hakan ya zama dole domin hana shugabannin kasar na gaba amfani da ikonsu ta yadda bai kamata ba wajen janyo yaki.

Sanatoci sittin da shida ne suka goyi bayan sauyin yayin da talatin suka ki.

A karkashin kundin tsarin mulkin Amurka, majalisar dokokin kasar ce kawai take da ikon ayyana shigar kasar yaki.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like