Majalisar Dattijai Tayi Watsi da Sunan Magu.


Ibrahim-Magu

Majalisar dattijai tayi watsi da sunan Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC. Wannan ne dai karo na biyu da majalisar ta dattijai ke watsi da sunan Magu.

Watsi da sunan da majalisar tayi ya biyo bayan wasikar da ta samu daga hukumar tsaro ta farin kaya DSS, wacce ta kara jaddada matsayinta kan zargin da a keyi masa.

A zaman tantancewar na yau Sanata Dino Melaye dan jamiyar APC daga jihar Kogi yayi nuni ga wasikar da majalisar ta karba daga hukumar ta DSS jiya da misalin karfe biyar na yamma.

” Mai girma shugaban EFCC ina sonka Kuma na yaba da dumbin tunaninka da iliminka, a gabana ina dauke da rahoto biyu daga SSS wanda aka turowa majalisa cikin watan oktoba na shekarar 2016 daya kuma majalisa ta same shi ne jiya da karfe biyar na yamma.

Bayan duba na tsanaki ga rahoton, rahoton farko ya sameka da laifi amma sugaban kasa ya sake tsaben ka. Melaye yace

A sabon rahoton da hukumar ta DSS ta turawa da majalisar, tace a binciken da tayi Magu bashi da gaskiya da rikon amana, saboda haka in har aka nada shi shugabancin hukumar to zai kawo nakasu a yakin da ake yi da cin hanci da rashawa.

Galibin Sanatocin majalisar sun goyi bayan abinda rahoton ya kunsa.

 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like