Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da kai agaji Borno


 

 

Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da aikin kai kayan agaji ga mutanen dake fuskantar yunwa a Jihar Barno, sakamakon harin da  kungiyar Boko Haram ta kai kan tawagar motocin hukumar.

Wata sanarwa da hukumar UNICEF ta bayar ya nuna cewar jiya aka abkawa tawagar motocin kungiyar bayan sun kai kayan agaji Bama suna komawa Maiduguri, kuma cikin wadanda aka raunana harda jami’in kungiyar da na hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya.

Kakakin rundunar sojin Najeriya kanar Sani Usman Kukasheka ya tabbatar da harin, inda yace cikin wadanda aka raunana harda jami’an su guda uku.

Dubban mutane ke fuskantar tsananin rashin abinci a Yankin kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar agaji ta Medicins San Frontier suka sanar.

You may also like