Majalisar Dinkin Duniya Tayi Kira Da A Zauna Lafiya Kan Wa’adin Ficewa Daga Arewa Da Aka Bawa Al’ummar Kabilar Igbo 


Majalisar Dinkin Duniya,tayi kira ga kabilu daban-daban, da kuma kungiyoyi da suke a kasarnan da su kasance masu hakuri da juna domin samar da hadin kai da kuma zaman Lafiya a kasarnan.

Wakilin majalisar a Najeriya, Edward Kallon, ya bayyana haka lokacin da yake mai da martani kan wa’adin da wasu matasan arewa suka bawa al’ummar kabilar Igbo da su fice daga yankin Arewa, kafin ranar daya ga watan Oktoban wannan shekarar. 

 “Dole ne muyi aiki tare cikin zaman lafiya  wajen warware damuwar da kowanne bangare na kasar nan ke da ita,”  kallon yace a sanarwar da yafitar. 

“Nayi farin ciki da martanin da shugabannin suka mayar daga ko ina cikin Najeriya inda suka yi allawadai da wa’adin.”

Wakilin na majalisar dinkin duniya yayi kira ga shugabannin gargajiya dana addini da suyi fadakar da matasa kan yadda zasu warware rikici cikin ruwan sanyi. 

Ya kuma yabawa  gwamnatin tarayya, gwamnatocin jihohi, matasa, shugabannin kungiyoyin fararen hula,  jami’an tsaro, shugabannin addini kan kokarinsu na tabbatar da zaman lafiya.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like