Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewar zata gudanar da bincike kan yadda aka ci zarafin bil-Adama a sassa daban daban na kasar Mali.
Majiyar dakarun wanzar da zaman lafiya da sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali {MINUSMA} ajiya Asabar ta sanar da cewa: Tawagar Majalisar Dinkin Duniya zata gudanar da bincike kan yadda kungiyoyi da suke dauke da makamai suka ci zarafin bil-Adama a sassa daban daban na kasar Mali bayan gano wasu tarin manyan kabarurruka a kasar.
Majiyar ta kara da cewa: Bangarorin da suke dauke da makamai sun aiwatar da kashe-kashen gilla kan jama’a a kokarin da suke yi na samun nasarar mamaye yankunan kasar. Kamar yadda ana nuna yatsar zargi kan cin zarafin bil-Adaman ne kan tsoffin kungiyoyin ‘yan tawayen kasar da suka yi yunkurin kafa sabuwar kasar Azwad a yankunan arewacin kasar Mali da kuma kungiyoyin sa-kai da suke goyon bayan gwamnatin Mali a gumurzun da suka yi a watan Yunin shekara ta 2015.