Majalisar dokokin jihar Kano ta tantance tsohon shugaban jam’iyar APC a matsayin kwamishina


Majalisar dokokin jihar Kano a wani zaman gaggawa da tayi ranar Alhamis ta amince da zaɓen da akayi wa Alhaji Abdullahi Abbas tsohon shugaban jami’iyar APC ɓangaren gwamna Abdullahi Ganduje don zama kwamishina a majalisar zartarwa ta  jihar.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje shi ne ya mika sunan shugaban jam’iyar gaban majalisar domin amincewa da shi, cikin wata wasika da shugaban majalisar Yusuf Abdullahi Ata ya karanta wanda ya jagoranci zaman majalisar.

Yan majalisar bayan wani kuduri da mataimakin shugaban majalisar, Hamisu Chidari,  ya gabatar inda ya nemi ya nemi su amince  da shi duba da irin gudunmawar  da ya bayar wajen cigaban  jam’iyar APC dama jihar Kano baki ɗaya lokacin da yake shugabancin jam’iyyar APC , dukkanin yan majalisar sun amince da kudirin na cidari.

Abbas ya kasance kwamishinan muhalli a gwamnatin tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso.

Da yake magana bayan kammala tantancewar Abbas yayi alƙawarin aiki tare da dukkanin ya’yan jam’iyyar dake majalisar zartarwa domin cigaban jihar baki daya.

You may also like