Majalisar kasa ta bukaci a buga karin sabobbin kudi ko kuma a maido da tsofaffiCBN

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto,

Majalisar ta kunshi tsofaffin shugabannin Najeriya da shugabannin majalisar dattawa da wakilai da wasu ministoci da kuma gwamnonin kasar.

Majalisar magabata ta kasa a Najeriya wato Council of State, ta kammala wani taron gaggawa a fadar shugaban kasar da ke Abuja inda ta bukaci babban bankin kasar, CBN ya samar da karin sababbin takardun kudi domin amfanin al’ummar kasar.

A cewar majalisar, idan sababbin kudin ba za su samu ba, to CBN ya koma bai wa jama’a tsofafun takardun kudin.

Majalisar – wadda ke karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari – ta kira taron ne domin tattaunawa ka halin da kasar ke ciki a yanzu da ta ke tunkarar babban zabe.

Majalisar ta kunshi tsofaffin shugabannin Najeriya da shugabannin majalisar dattawa da na wakilai da wasu ministoci da kuma gwamnonin kasar.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like