Majalisar Malaman Kano Ta Amince Da Hukuncin Rataye Abduljabbar Kabara
Kimanin shekara guda da rabi aka kwashe ana gwabza wannan shari’a a gaban babbar kotun shari’ar Musulinci ta Kano, tsakanin lauyoyin gwamnati da na wanda ake tuhuma da aikata wannan laifi, wato Malam Abduljabbar Nasiru Kabara.

A ranar alhamis ne kotu karkashin jagorancin mai shari’a Sarki Abdullahi Yola ta yanke hukuncin kisa ga Malam Abduljabbar Nasiru Kabara, ta hanyar rataya bayan tabbatar da laifin furta kazaman kalamai da kuma alakanta su da Annabin Rahama Muhammad S.A.W.

Yanzu haka dai kungiyoyin Musulinci a Kano na ci gaba da tofa albarkacin bakin su da kuma daukar matsaya dangane da wannan hukunci.

A yayin wani taron gaggawa da marecen jiya Juma’a, mambobin zauren hadakar Malaman Kano, wadda ya kunshi dukkanin darikun addinin musulinci a Kano, ya tattauna akan wannan hukunci kuma ya yabawa kotun bisa kokarinta na tabbatar da adalci.

Dr Sa’idu Ahmad Dukawa sakataren zauren hadakar malaman Kano, wanda ya fitar da sanarwar bayan taro, yace mambobin zauren sun bayyana farinci dangane da wannan hukunci tare da godewa alkalin kotun da lauyoyin gwamnati da suka jajirce da sauran masu ruwa da tsaki.

Shi-ma Malam Bashir Adamu Aliyu na Cibiyar bunkasa harkokin Islama ta Najeriya wato Islamic Forum of Nigeria yace kwantar da hankalin da al’umar musulmin Kano sukayi zuwa lokacin da kotu ta kammala shari’ar ya taimaka wajen cimma nasara da adalci.

Baya ga hukuncin kisa ta Hanyar rataya, babbar kotun shari’ar musulincin ta Kano ta umarci gwamnati ta rufe msallatan Malam Abduljabbar dake unguwanni shara da Gwale a cikin birnin Kano tare da haramta sanya karatuttukan sa a kafofin yada labarai.

Sai dai masana shari’a sunce malamin nada kwanaki 30 ya daukaka kara, muddin yana muradi, amma idan bai yi hakan ba gwamnati zata zartar da hukuncin bayan karewar wa’adin.

Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Kwari cikin sauti:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like