Majalisar Ministoci Ta Amince Da Kafa Sabuwar Jami’ar Rundunar Soja


A zaman da majalisar ministoci ta yi a jiya a karkashin Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osibanjo, ta amince da kafa wata sabuwar jami’a ta rundunar Sojan Nijeriya.

Da yake karin haske kan zaman majalisar, Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya ce za a kafa jami’ar ce a garin Biu da ke jihar Borno. A halin yanzu dai, rundunar tana amfani da kwalejin horas da manyan hafsoshinta da ke Kaduna (NDA) ne wajen bayar da shaidar kammala digiri.

You may also like