Majalisar Tarayya ta gayyaci Buhari kan Tattalin arziki


2015-12-16t154410z_256291546_gf10000267779_rtrmadp_3_nigeria-politics

 

Majalisar Dattijai da ta wakilan Tarayya sun bukaci shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana a gabansu domin gabatar da jawabi kan dubarun da gwamnatin shi ke bi na fitar da Najeriya daga kangin matsalar tattalin arziki.

Majalisun biyu na bukatar cikakken bayani ne daga shugaba Buhari akan matakan da gwamnatin shi ke dauka domin magance matsalolin tattalin arzikin da Najeriya ta shiga, musamman faduwar darajar Naira da ya haifar da tsadar kayayyaki da kuma yadda matsalar ta shafi rasa aikin yi.

Tun da farko Majalisar Dattijai ta amince da wani daftari mai kunshe da hanyoyin bunkasa ayyukan noma tare da taimakawa Najeriya karkatar da tattalin arzikinta daga dogaro da arziki fetir.

Zuwa yanzu dai fadar Shugaban kasa ba ta amsa cewa ko Buhari zai bayyana a gaban ‘Yan Majalisun ba.

You may also like