Majalisar Tarayya Za Ta Gayyaci Shugaba Buhari Kan Batun Tattalin Arzikin Nijeriya


buhari-saraki-dogara

 

Majalisar tarayya ta aike da wata gayyata ga shugaba Muhammadu don halartar wani gamayyan zaman majalisun biyu (dattijai da wakilai) don bayyana musu yadda majalisar zartarwa ta tsara yadda za ta fid da kasar daga halin tabarbarewar tattalin arzikin da ta ke ciki

An cimma wannan matsaya a zaman majalisar dattijai na yau, inda majalisar ta amince da shawarar da majalisar wakilai ta bayar na su gayyaci shugaban kasa ya zo gabansu don yi musu bayanin yadda ya ke shirin fidda Nijeriya daga cikin halin da ta ke ciki

Kafatanin ‘yan majalisar ta dattawa sun amince da kudirin a lokacin da shugaban majalisar Bukola Saraki ya tambayesu kan batun amincewar da kudirin ko rashin amincewar

“Masu girma abokan aiki, shin kun aminta da kudirin majalisar wakilai na mu gayyaci shugaban kasa Muhammadu Buhari don ya yi mana bayani, a wani zama na gamayyar majalisun, tsare-tsaren da gwamnati ta ke yi na fid da Nijeriya daga halin da ta ke ciki?”

Wadanda suka aminta da wannan kudiri su ce ‘Aye’!!! Wadanda kuma ba su aminta ba su ce ‘Nay’. Kamar dai yadda ya ke a al’adar majilisar.

inda ‘yan majalisar gaba daya suka amsa da ‘Aye’. Shi kuma shugaban majalisa ya tabbatar da cewa masu ‘Aye’ sun lashe.

Sai dai, har zuwa lokacin da aka tashi daga zaman majalisar ba a bayyana ranar da za a gayyaci shugaba buhari wannan zama ba.

In ba a manta ba, majalisar wakilai ce gabatar da wannan kudiri a ranar Alhamis 22 ga watan Satumba da mafi girman rinjaye inda majalisar ta wakilai ta turowa majalisar dattijai don ta tabbatar da kudirin kamar yadda dokar kasa ta tanadar

Tun dai bayan dawowar majalisun daga dogon hutun da suka tafi ne suka shiga aiki ka’in da na’in wajen ganin sun taimaka an cire kasar daga halin tabarbarewar tattalin arziki

Cikin abubuwan da majalisar dattijai ta yi na ganin an fidda jaki daga duma kuwa sun hada da yin wasu zama har kwanaki biyu a jere tare da fitar da shawarwari har guda 20.

Muhimmai daga shawarwarin kuwa sun hada da: Kada kasar ta kuskura ta sayar da kadarorinta kamar yadda wasu ke ta baiwa gwamnati shawara.

Majalisar ta dattijai har lau ta bayar da shawarar a yi wa sashen kundin mulkin Nijeriya na 162 gyara wanda ya yi magana akan yadda ake rarraba arzikin kasa tsakanin gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi

You may also like