Majalisar wakilai na son zaɓen shugaban ƙasa ya zamo na ƙarshe a jerin jadawalin zaɓen ƙasa


Zaɓen shugaban ƙasa shine zai kasance na ƙarshe a jerin jadawalin babban zaɓen ƙasa kamar yadda wani gyaran dokar zaɓen ƙasa da majalisar wakilai ta tarayya ta yi ya nuna.

Zaɓen yan majalisun tarayya shine zai zamo na farko a jadawalin sai kuma zaɓen gwamnoni tare da yan majalisun jihohi ya biye masa baya.

Dukkannin hakan da ma wasu gyare-gyare na kunshe ne cikin gyaran dokar zaɓe ta shekarar 2010 da majalisar wakilai ta tarayya tayi a zamanta na jiya Talata.

A yanzu dai yadda tsarin yake ana fara zaɓen shugaban ƙasa dana ƴan majalisun tarayya rana ɗaya kana a yi na gwamnoni da na ƴan majalisun dokoki na jihohi rana guda.

Lokacin da take amincewa da rahoton kwamitinta kan harkokin zaɓe da kuma Jam’iyun siyasa majalisar ta kuma ƙara yawan kuɗaɗen da ɗan takarar shugaban ƙasa zai iya kashewa a yaƙin neman zaɓe daga biliyan ₦1 kamar yadda yake a yanzu zuwa biliyan ₦5 na gwamna kuma daga miliyan ₦200 zuwa biliyan ₦1.

Wani gyaran kuma da aka yi kan  sashi na 36 na dokar zaɓen zai bawa mataimakin ɗan takara damar gadon kuriun da ɗan takarar da ya mutu ana tsaka da kaɗa kuri’a  kafin a kammala zaɓe.

Dukkanin gyararrakin da majalisar ta yi  baza su  zama doka ba har sai sun yi dai-dai da na majalisar dattawa kana shugaban kasa Muhammad Buhari ya sa musu hannu.

You may also like