Majalisar wakilai ta bukaci a kara kudin harajin taba sigari


Majalisar wakilai ta tarayya  a ranar Alhamis ta amince da kudirin dake bukatar kara harajin da ake karba kan taba sigari domin rage bazuwarta da kuma samar da kudin kiwo lafiya.

Amincewa da karin ya biyo bayan kudirin da dan majalisa, Sergius Ogun, dan jam’iyar APC daga jihar Edo ya gabatar kan hatsarin dake tattare da shan taba sigari ga lafiyar jikin dan adam da kuma muhalli.

Bayan da majalisar ta amince da kudirin ta umarci kwamitinta kan harkokin kudadi da ma’aikatar kudi domin su duba harajin taba  da ake biya.

 Haka kuma majalisar ta umarci kwamitinta kan harkokin lafiya da ya tabbatar an aiwatar da kudirin kana ya kawowa majalisar rahoto cikin watanni shida.

Majalisar ta kuma shawaraci gwamnatin tarayya kan ta fara wani gangamin fadakarwa domin rage amfani da tabar da kuma daukan kwararan mataki  na taikata tallata taba sigari.

Haka kuma ta shawarci gwamnatin da aiwatar da tsarin da ya hana shan taba a bainar jama’a musamman wurare mallakin gwamnati.

Tun farko da yake gabatar da kudirin, Ogun yace maganar da ta shafi taba sigari na cigaba da jan hankalin kasashe daban-daban na duniya.

Dan majalisar ya ce shan taba sigari na jawo mutuwar mutane  7 a duniya baki daya a ko wace shekara.

Ya ce a Najeriya akwai kiyasin dake nuna cewa akwai mutane miliyan 5 dake shan taba sigari wadanda suke saka kimanin mutane miliyan 30 da basa shan tabar cikin hatsari.

You may also like