Majalisar wakilai ta nemi shugaba Buhari ya bayyana a gabanta


Majalisar wakilai ta gayyaci shugaban kasa Muhammad Buhari kan yawan kashe-kashe dake faruwa a kasar nan.

Majalisar ta yanke shawarar gayyatar shugaban kasar ne ya yin zamanta na ranar Laraba.

Yan majalisar sun nemi shugaban kasar ya bayyana a gabansu domin ya yi bayani kan halin da sha’anin tsaron kasarnan ke ciki.

Amma kuma yan majalisar basu bayyana ranar da ake sa ran shugaban zai bayyana ba. Haka kuma yan majalisar sun kada kuri’ar rashin goyon baya ga shugabannin rundunar sojin kasarnan kan gazawar da sukai na kawo karshen kashe-kashen.

Har ila yau kuma sun yanke shawarar dakatar da zaman majalisar kwanakin zama uku domin nuna adawarsu ga kisan.

Daukar matakin ya biyo bayan kudirin da Mark Gbilla wakili,daga jihar Benue ya gabatar kan harin ramuwar gayya da sojoji suka kai kan wani gari dake jihar.

You may also like