Majalisar wakilai ta umarci a kai gwamnan CBN gabanta ranar TalataGbajabiamila

Asalin hoton, OTHERS

Majalisar wakilan Najeriya ta umurci babban sufetan ‘yan sandan kasar ya kai mata gwamnan babban bankin kasar nan da ranar Talata mai zuwa.

Majalisar ta yanke wannan hukuncin ne bayan ta gayyaci gwamnan babban bankin har sau biyu ba ya zuwa.

Wani rahoto na cewa ‘yan majalisar suna so ne su ji daga bakin gwamnan dalilin da ya sa ba za a kara wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun naira ba, wadanda bankin ya ce za su daina aiki daga ranar 31 ga wannan wata na Janairu.

‘Yan majalisar sun kai har wuya ne sakamakon gazawar gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele wajen bayyana a gaban wani kwamiti na musamman da majalisar wakilan ta kafa.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like