Majalisar wakilai zata binciki rashin biyan ma’aikata albashi a jihar Kogi


Majalisar wakilai ta tarayya ta umarci kwamitinta na wucin gadi kan kudaden tallafi da aka bawa jihohi da ya binciki rashin biyan albashi a jihar Kogi kana ya kawowa majalisar rahotonsa cikin mako guda.

Haka kuma majalisar ta umarci Babban Bankin Najeriya CBN da yaba ta rahoton yadda aka yi amfani da tallafin kudin biyan albashi da aka bawa jihohi.

Umarnin ya biyo bayan amincewa da gagarumin rinjaye kan kudirin da ke bukatar kulawar gaggawa da dan majalisa, Sunday Karimi, na jami’iyar PDP daga jihar Kogi ya gabatar a zaman majalisar na ranar Talata wanda kakakin majalisar Yakubu Dogara ya jagoranta.

Da yake gabatar da kudirin, Karim, ya ce duk da kason wata-wata na asusun tarayya, tallafin kudin biyan albashi da kuma biyan bashin kudin Paris Club da jihar Kogi ta karba, har yanzu matsalar biyan albashi ga ma’aikatan jihar na cigaba da yin ƙamari.

Ya ce Mista Edward Soje, Darakta a Hukumar Ma’aikatan Jihar ya hallaka kansa saboda gaza sauke nauyin da yake kansa da yayi a matsayinsa na magidanci mai iyali.

Dan majalisar ya ce marigayin ya hallaka kansa bayan da maidakinsa ta haifa masa yan uku a wani asibiti dake Abuja .

Ya kara da cewa marigayin na bin bashin albashin wata 11 wanda hakan yasa zai yi wuya ya  iya sauke nauyin da ake kansa.

Ya kara da cewa irin wannan hali da Soje ya ke ciki shine halin da ma’aikatan jihar suke ciki da ma yan fansho.

Bayan amincewa da kudirin majalisar ta shawarci gwamnatin tarayya dama na jihohi kan su bada fifiko wajen biyan albashi.

You may also like