Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da daftarin kasafin kudin shekarar 2018


Majalisar zartarwa ta tarayya a yau Alhamis ta  amince da daftarin kasafin kudin shekarar 2018.

Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare, Udom Udoma, ya sanar da manema labarai haka bayan kammala taron majalisar zartarwa ta yau da shugaban kasa Muhammad Buhari ya jagoranta.

Ministan ya ce bangaren zartarwa zai hada kai da ɓangaren majalisar ƙasa domin yadda da ranar da shugaban kasa Muhammad Buhari zai gabatarwa da majalisar daftarin kasafin kudin.

Udoma ya ki amincewa ya bayyana cikakken bayanin kasafin kudin.

Ya ce bangaren zartarwa ya cika alkawarin da yayi na tabbatar da an kammala aikin daftarin kasafin kudin cikin watan Oktoba.

You may also like