Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da karin biliyan ₦7.7 na kwangilar Madatsar Ruwa dake Mangu


Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince  da kara kudin aikin gina Madatsar Ruwa dake Mangu a jihar Plateau daga naira biliyan ₦5.66 zuwa biliyan ₦7.66.

Garba Shehu,mai magana da yawun shugaban kasa,shi ne ya bayyana haka sa’ilin da ya ke wa manema labarai jawabi a fadar shugaban kasa bayan kammala taron majalisar zartarwar na yau.

Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce haka ne ya kawo jumullar kudin kwangilar ya kama biliyan ₦13.2

Haka kuma majalisar ta amince da karin kudin gyaran Gadar Marina da ta kone da kuma aikin kula da gadar Eko dukkaninsu dake Lagos da kamfanin Build Well Plant and Equipment Industries Limited zai gudanar.

You may also like