Majalissa ta bada Umarnin Cafke Shugaban Kwastan


Majalisar Wakilai ta yi barazanar bayar da umarnin kama Shugaban Hukumar Kwastan na Kasa, Kanal Hamid Ali bisa kin bayyana gaban kwamitin majalisar wanda ke bincike kan yadda hukumar ta biya milyan 250 ga wani kamfanin insora na bogi.
Shugaban Kwamitin bincike na majlisar, Hon. Adenkunle Abdulkabir ne ya tabbatar da haka inda ya nuna cewa, sau biyu Shugaban Kwastan din ya ki mutunta gayyatar su a maimakon haka sai ya turo Mataimakinsa, Austin Warikoru a matsayin wakilin sa. Ya ce sun gano wasu makudan kudade da hukumar ta biya ga wasu kamfanonin insora na bogi.

You may also like