Majalissa Ta Dakatar Da Dokar Hana Shigowa Da Motoci Ta IyakaA jiya, Laraba ne, Majalisar Dattawa ta dakatar da sabuwar dokar nan wadda ta haramta shigo da Motoci ta iyakokin Nijeriya .
A shekarar da ta gabata ne, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa daga ranar 1 ga watan Janairu na shekarar 2017, ta haramta shigowa da Motoci ta Iyakoki sai ta hanyar tashar jiragen ruwa. 

Sai kuma gwamnatin ta tsawaita wa’adin da watanni uku don bayar da dama ga dillalan Motoci su shigo da sauran motocin da suka makale a Iyakoki bayan cikar wa’adin farko.

You may also like