Watanni biyar kenan tun bayan da Shugaba Muhammad Buhari ya gabatar wa majalisar Dattawa bukatar neman tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin cikakken Shugaban hukumar EFCC.
Wata majiya daga Fadar Shugaban kasa taTabbatar da cewa Buhari ya nuna rashin Jin dadinsa kan yadda majalisar ta jinkirta bukatar da tabbatar wa Magu shugabancin EFCC inda ya alakanta matsayin majalisa kan wasu tsiraru da ke neman gurgunta yaki da rashawa.
Rahotanni sun nuna cewa akalla sanatoci Tara ne hukumar EFCC ke tuhuma da laifin rashawa ba ya ga Uwargidan Shugaban majalisar, Toyin Saraki. Sai dai ana sa ran Buhari zai sake tuntubar Saraki kan bukatar.