Majalisar tarayya ta mikawa Shugaban Kasa kudirin garambawul da ta yiwa dokokin zabe wanda a ciki ta canja ranar da za a gudanar da zaben Shugaban kasa don neman amincewarsa.
A makon da ya gabata ne, majalisar ta shiga cikin rudani bayan da wasu sanatoci suka fice daga zauren majalisar saboda nuna adawa ga matakin canja ranar zaben Shugaban kasa ta yadda zai zama na karshe bisa zargin cewa an canja ranar ce don ganin Buhari bai lashe zaben ba.