Majalisar Dattawa ta tabbatar da rahotannin da ake yayatawa inda ta nuna cewa ta sayo mota mai sulke a kan Naira Milyan 49.1 saɓanin Naira milyan 298 da ake ta yayatawa.
Kakakin Majalisar, Sanata Sabi Aliyu Abdullahi ya ce a shekarar da ta gabata ne aka sayo motar a lokacin da ake musayar Dalar Amurka a kan Naira 165. Ya ce lokaci ya yi da mutane za su tantance rahoto kafin su rika yayatawa.