Majalissa tayi Watsi Da Bukatar Buhari Na Karbo Bashi 


Majalisar Dattawa ta ki amincewa da bukatar da Shugaba Muhammad Buhari ya gabatar mata na amince masa ya karbo bashin dala Bilyan 29.96 don aiwatar da manyan ayyukan raya kasa.
Haka ma, ‘ya’yan majalisar sun nuna kin amincewa da sunayen jakadun da Buhari ya gabatar sai dai kuma Shugaban Majalisar, Bukola Saraki ya yi amfani da ikonsa wajen tabbatar da sahihancin wadanda aka tantance.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like