Majalissa Za Ta Binciki Sanatocin Da Ke Kulla Maƙarƙashiyar Tsige Saraki


Majalisar Dattawa ta fara binciken wasu sanatoci da ake zargin suna da hannu wajen makarkashiyar da ake kullawa na tsige Shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Bukola Saraki.

Tun da farko dai, an zargi Sanata Adamu Abdullahi daga jihar Nasarawa da shirya zanga zangar adawa da shugabancin Sanata Saraki inda dan majalisar Dattawa mai wakiltar jihar Ebonyi ta Tsakiya, Sanata Obinna Ogbo ya ce yana da cikakken shaida wanda ke alakanta Sanata Adamu da wannan yunkuri na tsige Saraki.

You may also like