Majalissar Ƙolin Najeriya Ta Amince Da Narka Naira Bilyan 360 A Harkar Noma


A zaman da Majalisar koli ta kasa ta yi a jiya Alhamis a karkashin jagorancin Shugaba Muhammad Buhari ta amince da shirin gwamnatin tarayya na saka Naira Bilyan 360 ga harkar noma da kiwo.

Da yake karin haske kan zaman majalisar, Gwamnan jihar Ogun, Bikunle Amosun ya ce, majalisar ta amince da wannan matakin ne don zaburar da tattalin arzikin Nijeriya.

You may also like