Majalissar Dattawa Ta Tafi Hutun Karshen ShekaraBayan da Majalisar dattawa ta rantsar da sabbin sanatoci guda uku da suka samu nasara a zabukan da aka gudanar a jihar Ribas, idaga bisani kuma ta tattara inata- inata ta tafi hutun karshen shekara wanda ba za ta dawo ba sai 10 ga watan Janairu, 2017.
Shugaban majalisar Bukola Saraki ne ya jagoranci rantsar da sabbin sanatocin yayin zaman majalisar a ranar Alhamis 15 ga watan Disamba.
Biyu daga cikin sabbin sanatocin ‘yan jam’iyyar PDP ne, yayin da jam’iyyar APC take da guda daya.

You may also like