Sai da ya aika musu da kwamitin cin bashi na kasa suka yi musu bayanin bukatar kudin da Najeriya ke yi
Buhari ya ce bashin da zai ciwo za’a yi amfani da shi ne wajen cikasa kasafin kudin 2017 sannan kuma ayi amfani da ragowar a biya wasu basussukan da ake bin Najeriya wadanda lokacin biyan su ya yi.
Da farko sun ki yarda, sai da ya aika musu da Kwamitin cin bashi na kasa, wanda har da ministan sufuri, Rotimi Ameachi, suka je majalisa a ranar 19 Oktoba suka yi musu bayanin bukatar wannan bashi da Najeriya ke yi.
Shehu Sani, Kaduna-APC, wanda har da shi a kwamitin cin bashin, ya ce bashin zai bude kafofin bunkasa tattalin arziki kuma zai samar da aiyukan yi ga al’ummar Najeriya, saboda har kamfaninnika masu zaman kan su zasu iya zuwa a basu bashi.