A zamanta na yau Laraba, majalisar dattijan Nijeriya ta tabbatar da Mai Shari’a Walter Onnoghen a matsayin alkalin alkalan Nijeriya ba tare da wata hamayya ba.
An haifi Onnoghen a ranar 22 ga watan Disambar 1950 a garin Okurike da ke karamar hukumar Biase ta jihar Cross Rivers.
Onnoghen ya yi nasarar zama alkalin kotun koli ta kasa tun a shekarar 2005 kuma ya kasance a kujerar riko na alkalin alkalai tun bayan barin aikin Mai Shari’a Mahmud Mohammed a watan Nuwamban 2016.
Onnoghen ya samu amincewar kwamitin shari’a ta kasa a watan Nuwamba don zama alkalin alkalai amma gwamnati ba ta tabbatar da shi ba sai yau.