Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci kasashen China, Amurka, Korea ta Arewa, Masar, India, Iran, sai kuma Isra’ila da Pakistan da su rattaba hannu kan yarjejeniyar haramta amfani da makamin Nukiliya.
Mambobin kwamitin tsaron 14 suka amince da wannan bukata amma ba tare da barazanar hukunta duk kasar da taki amsa kiran ba
Akalla kasashe 160 ne suka sa hannu kan yarjejeniyar haramta amfani da makamin Nukiliya a shekara ta 1996, kuma daga waccan lokaci zuwa yanzu kasashen Pakistan, India da kuma Korea ta Arewa sun gudanar da gwajin makamin na Nukiliya.
Sai dai kasar Korea ta Arewa ta maida martani kan bukatar, inda ta ce zata cigaba da gwaji tare da inganta makaman nukiliyar, domin ta haka ne kawai zata kare kanta daga duk wata barazanar tsaro.