Majalissar Dokokin Jihar Kebbi Ta Nemi Da A Damke DakingariMajalisar dokokin jihar Kebbi ta bayar da umarni ga Rundunar ‘yan sandan jihar kan ta kamo Tsohon Gwamnan jihar, Alhaji Usman Sa’idu Dakingari bisa kin mutunta gayyatar majalisar don yin bayani game da zargin ha’inci a wata kwangila da ya bayar a zamaninsa.

Kakakin Majalisar, Alhaji Sama’ila Kamba ya nuna cewa majalisar tana neman tsohon Gwamnan ne don ya fayyace yadda aka yi aringizon Naira Bilyan 6.4 a kan kwangilar filin saukar jiragen sama na jihar.

You may also like